Free

Wani Neman Jarumai

Text
From the series: A Jeren Zoben Mai Sihiri #1
Mark as finished
Font:Smaller АаLarger Aa

ANA IYA SAMU YANZU

FARETIN SARAKUNA

(Littafi na biyu a cikin zoben mai sihiri)



“ZOBEN MAI SIHIRI yanada dukan mahadan samun nasaran kwassam: kullekulle, akan kullekulle, al’ajabi, marasa soron bardawa, da soyayya masu ginuwa amma cike da ciwon zuciyoyi, yaudara da cin amana. Zai nishadantar da kai na sa’o i, kuma ya biya wa yara da manya bukata. An shawarci duk masu karatun fantasi su kasance dashi a dakin litafaffansu.”

--Sharhin litattafai da finafinai, Roberto Mattos


FARETIN SARAKUNA yakai mu mataki nagaba kan safarar Thor na muasamman zuwa zama namiji, yayinda yafara samun Karin fahimta akan shi waye, menene su baiwansa, yayinda ya kama hanyan zama gwarzo.


Bayan ya gudu daga kurkuku, Thor yaji soro daya gano wani kokarin kashe sarki MacGil. Da MacGil yamutu, masarautar ta shiga rudaniya. Yayinda kowa ke neman sarautan, haraban kara yakasancewa da rikicin cikin iyali, fadan neman iko, buririka, kishi, mugunta, da yaudara. Dole azabi magaji daga yaran, sai daddaden twakafin kaddara, tushin karfinsu, zai samu zarafin gwada dagashi daga wani sabon mutum. Amma ana iya juya wannan: an samo makamin kisan, kuma an hura wuta a kokarin wanda yayi kisan. A daidai wannan lokacin kuma dangin MacGil na fuskantan wani sabon barazana daga dangin McCloud, wadanda ke shirin kawo hari kuma daga cikin zoben.


Thor na kokarin dawowa da soyyayar Gwendolyn, amma watakila lokaci yakure: ance masa ya tattara, yashirya da yan’uwansa a makamai wa dajin, kwanaki dari masu cike da wahala da kowani dan runduna yakamata ya rayu bayansu. Yan rundunan zasu sallaka loton, waje da kariyar zoben, zuwa cikin waje wajen, kuma suyi safara su sallaka tekun Tartuvian zuwa tsibirin gajimare, wanda akace dodon dragon ne sintirinsa, domin kafu a mazakuta.


Ko zasu dawo? Zoben zata rayu a rashinsu? Kuma Thor zaizo yasan sirrin kaddararsa?


Da gwanintan gina duniya cikin labara da gina halayen mutane, FARETIN SARAKUNA hadadden labarin abokanai da masoya ne, na abokan hammaya da masoya, na gwanayen mayaka da dodunan dragon, na bukata da kulle kullen siyasa, na girma zuwa balaga, na karya soyyaya, rudi da buri. Labari ne na kamala da kokari, na sakamako da kaddara, na sihiri. Labarin fantasy ne mai kawo mu wani duniya wanda bazamu taba mantawa dashi ba, kuma wanda zai baiwa mutane masu kowani irin shekaru maza da mata sha’awa.


Littatafi na biyu zuwa na goma sha uku a jerin suna nan a kuswa yanzu suma!



Ka saurari jeren littafin ZOBEN MAI SIHIRI a karance!

Wasu littatafan da morgan rice ya wallafa


ZOBEN MAI SIHIRI

WANI NEMAN JARUMAI (LITTAFI NA DAYA)

PARETIN SARAKUNA (LITTAFI NA BIYU)

KADARAN SU (LITTAFI NA UKU)

KUKAR MAI GASKIYA (LITTAFI NA HUDU)

RANTSUWAN CIKAN BURI (LITTAFI NA BIYAR)

RATAYAN KOKARI A BAKIN DAGA (LITTAFI NA SHIDA)

BORIN TAKWUBA (LITTAFI NA BAKWAI)

YARDAN MAKAMAI (LITTAFI NA TAKWAS)

SAMAN DARIN SIHIRAI (LITTAFI NA TARA)

KOGIN ABUBUWAN KARIYA (LITTAFI NA GOMA

MULKIN BAKIN KARFE (LITTAFI NA GOMA SHA DAYA)

KASAR WUTA (LITTAFI NA GOMA SHA BIYU)

MULKIN SU SARAUNIYAI (LITTAFI NA GOMA SHA UKU)

RANTSUWAN YAN’UWA (LITTAFI NA GOMA SHA HUDU)


RAYUWAN ABUBUWA UKU

FILIN DAGA NA DAYA: MASU SHANYA BAYI A RANA (LITTAFI NA DAYA)

FILIN DAGA NA BIYU (LITTAFI NA BIYU)


LABARUN MAYU

AJUYE (LITTAFI NA DAYA)

SOYYAYE (LITTAFI NA BIYU)

WANDA A KA CI WA AMANA (LITTAFI NA UKU)

KADDARARE (LITTAFI NA HUDU)

BUKATACCE (LITTAFI NA BIYAR)

AURARRIYA (LITTAFI NA SHIDA)

RANTSATSE (LITTAFI NA BAKWAI)

SAMMAME (LITTAFI NA TAKWAS)

TARYAYYE (LITTAFI NA TARA)

BUKATTATE (LITTAFI NA GOMA)

KADDARRARE (LITTAFI NA GOMA SHA DAYA)

Bayani a kan Morgan Rice


Morgan Rice shine na daya a cikin marubuta da suka fi ciniki daya rubuta LABARAIN MAYU, wani jere na matasa daya kunshi lattafai goma sha daya (kuma kirgen bai saya ba tukuna); mafi cinikin jeren littatafan RAYUWAN ABUBUWA UKU, wani labarin hangen duniyar wata rana daya kunshi littatafai biyu (kuma kirgen bai saya ba tukuna); da kuma mafi cinikin na kololuwar jeren littatafan fantasi na ZOBEN MAI SIHIRI, mai littatafai goma sha uku (kuma kirgen bai kare ba tukuna).


A kan samu littatafan morgan a wallafe a takarda da kuma a karance da murya, kuma akwai tarjaman littatafain a harsunan jamus, faransa, italia, sipania, potugal, japanawa, sin, swedanawa, hollandia, turkiya, hungariya, cek da silovaniawa (wasu yarukan suna biyo wa a baya).


Morgan na da son yaji daga wurinka, saboda haka ka hanzarta ka ziyarci adireshinsa na yanar gizo a www.morganricebooks.com domin shiga jerin wasikun email, kasamu kyautan littafi, kasamu wasu kyaututuka na musamman, ka sauke na’urar wayoyi kyauta, kasamu labarai da dumiduminsu, ka sada zumunci a facebook da twitter kuma ka kasance kana sadarwa a koyaushe.