Free

Wani Neman Jarumai

Text
From the series: A Jeren Zoben Mai Sihiri #1
Mark as finished
Font:Smaller АаLarger Aa

Wani makamai zaka bukata, yallabai?” Thor ya tambaya.

Erec ya kalli kasa, yana kama da girmansa yakaru daga ta inda Thor ka kallonsa.

“Yana da wuya nasan ire iren yakin da zan samu a shekaran gabadaya. Amma ina bukatan na iya farauta, kuma na kare kaina. Saboda haka, ina bukatan doguwar takwafina. Kuma yakamata natafi da guntuwar takwafina ma, kwari, jakan baka, guntun mashi, kulki, wuka da kwangirin kariya na. ina ganin wadannan zasu yi.”

“To, yallabai,” Thor yace, sai ya balla cikin aiki. Ya gudu zuwa maratayin makaman Erec, a gefen dakin Lannin, ya binciki dozin dozin din makaman. Akwai ire iren makamai masu gamsara dayawa da za a iya zaba daga ciki.

Ya ciro makaman Erec ya lisafa duka ahankali, yana kawosu ma Erec daya bayan daya kuma yana mikasu wa Erec kokuma ya makala su a rigan kariyan dokin.

Yayinda Erec ya zauna a wurin yana daura safar saman hanunsa na fata, yana shirin tashi, Thor yagagara iya kallon tafiyarsa.

“Yallabai, ina jin aikina ne na raka ka a wannan tafiyan,” Thor yace. “Ni dan gindanka ne ai dama.”

Erec ya girgiza kai.

“Wannan tafiya ne da dole nayisa ni kadai.”

“To zan iya raka ka zuwa akalla sallakawan farko?” Thor ya danna. “Idan zaka nufi kudanci ne, akwai hanyoyi da nasani da kyau. Ni daga kudanci ne.”

Erec ya kalli kasa yana dubawa.

“Idan kana son ka rakani zuwa sallakawar farko, bana ganin wannan da damuwa. Amma tafiyan kan doki na yini daya ne mai wahala, saboda haka dole mutashi yanzu. Ka dauko dokin yan gidana, abayan dakunan dawakai. Mai launin kasan da jan gashin bayan wuya.”

Thor yakoma dakunan dawakan aguje yasamo dokin. Yayinda ya hausa, Krohn ya leko dakansa daga cikin rigarsa sai ya kalleshi a sama kuma yayi kuka.

“Babu damuwa, Krohn,” Thor ya tabbattar.

Thor yamike gaba, ya zunguri dokin domin yafara tafiya, sai ya bullo daga dakin dawakan. Erec baiyi wani jiransa ya iso ba lokacin das hi da Lannin suka ruga da sukuwa. Thor yabi Erec gwargadon ikonsa.

Sun tafi tare suka fita daga haraban sarki, ta mashigin, yayinda dayawan maso tsaro suka jashi yabudu sai suka saya a gefe. Dayawan yan Silver sun jeru, suna kallo, suna jira, sai yayinda Erec ke wucewa, suka daga hannayensu suka sara masa.

Tafiya agefensa ya karawa Thor kumburin kai, da zama dan gidansa, kuma yayi farin cikin rakashi, koda ma zuwa sallakawan farko ne.

Da shauran bayani dayawa da Thor keson yiwa Erec, abubuwa dayawa dayaso ya tambayeshi—kuma abubuwa dayawa dayakeson yamasa godiya akansu. Amma babu lokaci, yayinda dukansu biyu ke sukuwa suna nufan kudanci, suna bulla kan filaye, yanayin wurin nata sauyawa yayin da dawakansu rugawa hanyar sarki a cikin ranar karshen safiya. Yayinda suka wani tudu, daga can Thor na iya ganin duka yan runuduna a wani fili, suna karya bayansu yayinda suke tono. Thor yayi farin cikin rashin kasancewa cikinsu. Yayinda Thor ke kallo, yaga daya daga cikinsu ya saya yadaga hanu zuwagareshi. Gani nada dan wuya a cikin ranan, amma yaji tabbacin Kaman Reece ne yake sarawa. Thor ma yadaga hanu yayinda suka cigaba da tafiya.

Manyan hanyoyi masu kyau sun sauya da hanyoyin kauye marasa samun kula: rashin fadi, gargada, sai akarshe kusan basufi kananan hanyoyin da ba a bi akai akai masu yankawa cikin dajujjuka. Thor yasan nada hatsari wa mutanen kauya su bi wadannan hanyoyin su kadai—tumba ma daddare ba, da dukan barayi da suke afka musu, amma Thor bashi wani babban damuwa game da kansa, musamman ma da Ereca gefensa—kai ma inda dan fashi zai taresu ma, Thor naji ma shi dan fashin ne soron rayuwarsa. Dama, zai zama rashin hankali wa wani barawo ya gwada sayar da mutumin da yakasance dan Silver.

Sun yi tafiya kan dawakai gabadayan ranan, batare da hutawa ba, sanda Thor yagaji, numfashinsa na neman ya dauke. Yagagara yarda da irin juriyanda Erec ke dashi—duk da haka bai isa ya sanar wa Erec cewa yagaji ba, saboda soron kar yadaukeshi rago.

Sun wuce manyan maraban hanyoyi, kuma Thor ya iya ganesu. Ya san cewa idan suka cigaba da nufan dama, yai kawosu kauyensa. Na wani dan lokaci, Thor yaji tunanin gida ya mamayeshi, sai wani bangarensa yaso yabi hanyan, yaga mahaifinsa, kauyensa. Yayi tunanin komenene mahaifinsa kekanyi a yanzu, waye yake kiwon, yaya irin haushinda mahaifinsa yaji da bai dawo ba. Bawai ya damu dashi dayawa ba. Na wannan dan lokacin ne yakejin rashin abubuwanda da yasaba dasu. Yakasance, asali, asake cewa yagudu daga karamin kauyen, kuma wani bangarensa baya son ya taba dawowa.

Sun cigaba da sukuwa, da nisa akan nisa zuwa kudnci, zuwa yankunan da Thor bai taba zuwa ba. Ya taba jin masalakar kudanci, koda yake bai taba samun dalilin zuwa wurin dakansa ba, ya kasance daya daga cikin manyan masallaku uku dake zuwa karshen kudancin zoben. Yanzu yakasance sakaninsa da fadan sarki yakai tafiyan rabin wuni mai kyau, kuma rana yariga yayi sayi a sama. Thor, yana gumi, numfashi akare, ya fara tunani da soron ko zai iya komawa a cikin lokaci domin liyafan sarki na daren yau. Ko yayi kuskure ne daya raka Erec danisa haka?

Sun zaga wani saman tudu, sai akarshe thor yaganshi, a wurin a can inda Kaman sama ya hadu da kasa: bayanannen alaman masallakar farko. Ya alamantu da wani katon, siririn bele, tutar din sarki arataye akansa daga duka bangarori hudu, kuma yan Silver asaye suna saronsa asaman kananan dangan. Daga ganin Erec, gwanin mayakin dake sama ya busa algaitarsa. Ahankali, matarin mashigin yadagu.

Suna daidain dan yadi dari ne kawai, sai Erec ya rage gudun dokinsa zuwa tafiya. Cikin Thor ya kulle yayinda yagane cewa wadannan ne mintunansa na karshe da Erec kafin wani lokaci tsawo. Wayasani, azahiri, idan zai taba dawowa. Shekara daya lokaci ne mai sayi, kuma komai na iya faruwa. Thor yayi farin ciki, akalla, cewa shi yasamu wannan zarafin rakashi din. Yaji Kaman shi ya sauke hakkin dake kansa.

Su biyun na tafiya gefe da gefe, dawakansu na numfashi da karfi, mutanen na nufashi da karfi, yayinda suka nufi doguwar benen.

“Watakila bazan ganka na watanni dayawa ba,” Erec yace. “lokacin d azan dawo, zan kasance da amarya abiye dani. Watakila abubuwa su sauya. Koda yake komenene yafaru, kasani cewa zaka dinga kasancewa dan gidana ne.”

Erec yaja numfashi mai zurfi.

“Yayinda zan barka, akwai abubuwanda nakeson ka tuna. Ba a zama gwanin mayaki da karfi—amma da basira. Himma kadai baya mayar da mutum gwanin mayaki, saidai himma da mutunci da hikima ahade. Dole kayi aiki kulun domin gyara ruhunka. Hali nagari ba abaki yake ba—a aikace yake. Dole kayi aiki akansa, ka kara kaywun kanka, kowani lokacin kowani rana.”

“Acikin wadannan watanni, zaka koyi da amfani da duka nau’o’in makamai, duka irin iyawa. Amma katuna: akwai wani fuska gay akin mu. Fuskan mai sihiri. Ka nemi Argon. Ka koyi fitowa da boyayyun baiwanka. Na jisu ajikinka. Kanada babban haske a gabanka. Ba abin kunya bane. Ka fahimce ni?”

“Haka, yallabai,” Thor ya amsa, yana kumbure da godiya saboda hikimarsa da ganewansa.

“Na zabi na daukeka akarkashina saboda wani dalili. Kai ba Kaman shauran bane. Kanada kaddara mafi girma. Wanda yafi girma, watakila, akan nawama. Amma yakanse haryanzu bai tabbatta ba. Kada ka taba daukansa abin wasa. Dole ka cigaba da aiki akai. Domin zama gwarzon jarumi, ba zaka zama mara soro da mai iyawa ba kawai. Dole ka kasance da ruhun jarumi, kuma ka kasance da wannan akanka da zuciyarka akowani lokaci. Dole ka iya bada ranka domin wasu. Mafi girman gwanin mayaki baya neman dukiya ko girma ko yabo. Mafi girman gwanin mayaki dauki mafi wahalan dukan nema: neman ka mayar da kanka mai kara kyau a kowani lokaci. A kowani rana, dole kanemi Karin kyau. Ba fin shauran kyau ba kawai—amma kafi kanka kyau. Dole kanemi ka dauki damuwan wadanda basu kaika ba. Dole ka kare wadanda bazasu iya kare kansu ba. Ba nema ne na masu raunin zuciya ba. Name ne na gwarzaye,”

Zuciyan Thor nata juyawa yayinda yake shigar da bayanin duka, yana tunani akan kalmomin Erec ahankali. Ya rinjayu da godiya masa, kuma yagagara sanin yadda zai mayar da martini. Ya ji cewa zai dauki watanni kafin asalin bayanin ya shigeshi.

Sun kai mashigin masallakar farkon, suna kaiwa, dayawan ‘yan Silver sun fito domin gaisawa da Erec. Sun hauro wurinsa akan dawakai, manyan murmushi a fuskarsu, kuma yayin saukansa sonata buga masa hanu a baya, Kaman sofofin abokanai.

Thor ya sauko, ya karbi igiyan jan Lannin, sai ya jagoranceshi zuwaga mai lura da mashigin, domin ya ciyar ya kuma sefeshi. Thor yasaya a wurin yayinda Erec yajuya ya kalleshi, karo na karshe.

A sallamansu na karshe, Thor nada abubuwa dasukayi yawa dake son yafada. Yaso yagode masa. Amma kuma yaso yagaya masa komai. Da alaman. Da mafarkinsa. Da tsoronsa ma sarkin. Yayi tunanin watakila Erec zai fahimta.

Amma yagagara kawo kansa ga fada. Erec yariga ya kewayu da gwanayen mayaka, kuma Thor na soron Erec—da dukkansu—zasuyi tunanin ko ya haukace ne. Saboda haka yasaya a wurin, yayinda Erec ya mika hanu ya kamo kafadarsa wani karo na karshe.

“Ka kare sarkinmu,” Erec yace babu shakka.

Kalmominsa sun sa wani sanyi yah aura kashin bayan Thor, Kaman Erec ya karanci zuciyarsa.

Erec yajuya, yayi tafiya ta cikin mashigin tare da wasu gwanayen mayakan, yayinda suke wucewa, bayansu ajuya gareshi, sandunan karfen sun sauko ahankali.

Erec yatafi yanzu. Thor yaji wani rami a cikinsa. Watakila sai bayan shekara daya gabadaya kafin yagansa.

Thor ya dale dokinsa, yakamo igiyan jan, sai ya bugeta da karfi. Rana ya zo kuma yanada tafiyan rabin wuni mai kyau domin yasamu halartan liyafan. Yaji kalmomin Erec na karshe sonata dawowa a cikin kansa, Kaman wani maimaici.

Ka kare sarkinmu.

Ka kare sarkinmu.

SURA NA ASHIRIN DA TAKWAS

Thor na tafiya bias dokin acikin duhu, ya ruga cikin mashigin harabar sarki, kusan babu wani rage tafiyan dokinsa yayinda ya dire daga kansa, yana numfashi da karfi, kuma ya baiwa wani mai hidima igiyan jansa. Yakasance atafe bias dokin duk wunin yau, rana yafadi tun sa’o’i da suka wuce, kuma yana iya gani daga dukan hasken toci da ke ciki, yaji daga duk mafarkun bayan mashigin, cewa liyafan sarkin na cigaba. Yayi wa kansa fada domin kasancewa bayanan na irin wannan dogon lokacin, kuma yayi fata kawai cewa bai riga ya makara ba.

 

Ya ruga zuwa mai hidima mafi kusa.

“Komai na daidai a ciki?” ya tambaya agurguje. Dole yasani kosarki nanan da lafiyarsa—kodashike bazai iya tambayansa kaisaye ko an bashi guba ba.

Mai hidiman yakalleshi, yana mamaki.

“Kuma mai zai hana? Komai na daidai, sadai ka makara. Yan rundunan sarki yakamata su dinga zuwa akan lokaci. Kuma kayan ka sunyi dauda. Kana zaman mumunan misali acikin yan’uwanka. Wanke hannayenka, sai ka hanzarta ciki.”

Thor ya ruga ta mashigin, yana gumi, yasa hanayensa a wani karamin kwaryan dutse acike da ruwa, ya wasa afuskansa, ya zuba kan dogon kashinsa. Ya kasance yana tafe ne tun dasassafe, kuran kan hanya ya rufeshi, kuma yanaji Kaman ranaku goma ne suka hadu suka zama daya. Yaja numfashi mai zurfi, yayi kokarin kwantar da hakalinsa ya kuma nuna nitsuwa, sai ya taka da sauri ya gangara dakali bayan dakali, ya nifu manyan kofan zauren liyafan.

Yayinda yashiga ciki, ta manyan kofofi masu lankwashashen sama, yakasance Kaman yadda yake a mafarkinsa: agabansa akwai teburan liyafan guda biyu, akewaye da mutane. Surutun ya bugi Thor Kaman yanada rai, zauren a cike da mutane azahiri. Ba mutanen sarki, yan Silver day an rumduna kadai ke zaune a teburan liyafan ba, amma daruruwan wasu, matafiyan mawaka, kungiyoyin masu rawa, masu bada dariya, dozin dozin din mata daga gidajen karuwai… akwai har way au duka nau’o’in masu hidima, masu tsaro, karnuka sonata yawo aguje. Wurin yakasance da hayaniya.

Mutane sonata shan barasa daga manyan tuluna, kuma dayawansu nasaye, suna wakokin buguwa, arungume da juna, suna buga kofunansu da juna. Akwai ire iren abinci ashimfide akan teburan, aladun daji da barewa da duka nau’o’in namomin daji na gasuwa akan sanduna agaban wuta. Rabin dakin suna ci irin na handama, shauran kuma suna yawo suna hira a dakin. Kallon hayaniyan cikin dakin, ganin yanayin buguwan mutanen, Thor ya fahimci cewa daya iso da sauri fiye da haka, lokacinda aka fara, da nitsuwan yafi haka. Yanzu, a wannan makararen lokacin, yayi Kaman yazama Karin bukin bugaggu.

Martanin Thor na farko, bayan yin mamaki, shine sakewa mai zurfi dayaga sarki na raye. Yaja numfashin samun sauki. Yana lafiya. Ya sake tunanin ko wancan alaman bai nufi komai ba, ko mafarkinsa bai nufi komai ba. Amma duk da haka, yagagara ture yanayin da yakeji. Harwayau yanajin wani matsuwan son kaiwa ga sarki.

Ka kare sarkin mu.

Thor ya tutura hanyarsa zuwa cikin taron jama’a mai kaurin, yana kokarin bin dogwar hanyar dake kaiwa ga sarkin. Tafiyan baya sauri. Mutanen sun bugu kuma sun hargise, amake kafada da kafada, kuma MacGil na zaune daruruwan kafa daga can.

Thor ya lallaba yakai rabin hanya a sakanin taron mutanen sai ya saya, bazato ya hangi Gwendolyn. Tana zaune a daya daga cikin kanakanan tebura, dakenan daga gefeb zauren, akewaye da masu hidimanta. Tayi Kaman tanada damuwa, wanda ya bambamta da ainihin kamaninta. Abincinta da abinshanta sunanan bata tabasu ba, kuma ta koma gefe da zama, aware daga shauran yan dangin sarauta. Thor yayi tunanin ko wani damuwa ne yafaru.

Thor ya fice daga taron jama’an ya hanzarta zuwa gurinta.

Ta daga ido taganshi yana zuwa, amma maimakon tayi murmushi, Kaman yadda tasaba, fuskanta ya bakantu, a karo na karko, Thor yaga haushi a cikin idanunta.

Gwen ta tura kujeranta, ta tashi, tajuya bayanta, sai ta fara tafiya.

Thor yaji Kaman an soka masa wuka a zuciya. Yagagara gane martaninta. Ko yayi wani laifi ne?

Ya zagaya tebirin aguje, ya hanzarta zuwa gareta, ya kamo wuyan hanunta ahankali.

Ta bashi mamaki da wurgar da hanunsa, tajuya kuma tad aura masa fuska.

“Kada ka yarda ka tabani!” tayi ihu.

Thor ya jabaya da taku daya, martaninta ya girgizashi. Wannan Gwendolyn daya sani ne kuwa?

“Kiyi hakuri,” yace. “Banyi nufin cutar dake ba. Kuma ba raini ba. Naso nayi Magana dake ne kawai.”

“Bani da raguwan kalmomi maka,” tayi fushi, idanunta ahaskake da babban haushi.

“Maidakina, yi hakuri ki gaya mani, wani laifi na maki? Koda menene, tuba nakeyi.”

“Abinda kayi bazai magantu ba. Babu tubanda zai isa. Shine abinda ka kasance.”

Ta fara tafiya kuma, sai wani gefen Thor yayi tunanin yabarta, amma daya gefen yagagara tafiya kawai, ba abayan abinda ya shiga sakaninsu ba. Dole yasani—dole yasan dalilin dayasa ta tsaneshi dayawa haka.

Thor yayi gudu zuwa gabanta, ya tare mata hanya. Bazai barta ta tafi ba. Ba a haka ba.

“Gwendolyn, kiyi hakuri. Kiyi hakuri kawai ki bani dama daya domin nasan menene nayi. Kiyi hakuri, ki bani wannan kawai.”

Ta mayar da harara, tana haushi, hannaye akan kwankwasonta.

“Ina ganin ka sani. Ina ganin ka sani da kyau.”

“Bansani ba,” Thor yace da gaskiya.

Ta kalleshi, Kaman tana lissafinsa, sai daga karshe, tayi Kaman ya yarda da maganansa.

“Daren kafin rananda ka hadu dani, an gaya mani cewa ka ziyarci gidan karuwai. Cewa kasamu yadda kakeso da mata dayawa. Kuma kaji dadinsu dukan daren. Sai, yayinda rana yataso, lazo wurina. Wannan ya tunatar dakai? Ina kyaman halinka. Kyaman cewa nataba haduwa dakai, cewa kataba ni. Ina fatan bazan sake ganin fuskanka ba. Ka mayar dani wawuya—kuma babu mai mayar dani wawuya!”

“Maidakina!” Thor yayi ihu, yana koarin ya sayar da ita, yanason yayi bayani. Ba gaskiya bane!”

Amma wata kungiyan mawaka ta shiga sakaninsu, sai ta ruga ta tafi, ta zame cikin taron mutanen da saurinda yagagara samunta. Cikin dan lokaci, yarasa ta gaba daya.

Thor na konewa ta ciki. Yagagara yarda cewa wani yasameta, ya gaya mata karya akansa, yajuya tunaninta akansa. Yayi tunanin kowaye ne yayi wannan. Amma babu ma wani amfani yanzu; sakaninsa da ita yariga yabaci. Yafara mutuwa ta ciki.

Thor yajuya yafara tangal tangal adakin, yana tuna sarkin, yanajin babu wani abinda yarage masa, Kaman bashi da wani dalili na rayuwa kuma.

Kafun yaje nisan wasu kaffofi, babu sammani Alton ya bullo, yatare masa hanya, yana masa tsiya da wani murmushi. Yana sanye das afar kwafri na siliki, rigar velvet, da hula mai gashin tsunsu. Ya kalli Thor a kasa, da dogayen hancinsa da haba, kuma da mafi yawan girman kai da jiji da kai.

“To, to,” yace. “Idan bad an talakan bane. Kariga kasamu matan-aurenkan anan kuwa? Ai baka samu ba. Ina ganin gulma yariga ya bazu danisa dakuma fadi akan harkanka na gidan karuwai.” Yayi murmushi ya maso kusa, yanuna kananan, hakora masu launin kwai. “Kai, na tabbatta gulman yabazu.”

“Kasan abinda ake fada: idan akwai dan gaushin gaskiya, yakan tayar da gulma. Nasamu wannan gaushin. Yanzu kuma sunanka yabaci, yaro.”

Thor akumbure da haushi, abin ya isheshi. Ya taso sai ya naushi Alton a wuya, yaka dashi.

Bayan dan lokaci, mutane ne akansa, yan’uwansa a runduna, mayaka, suna raba su, suna jansu su rabu.

“Ka wuce kan iyankanka, yaro!” Alton yayi ihu, yana nuna masa yasa tasaman jikukkunan mutane. “Babu wanda yake taba dan gidan sarauta! Zaka ratayu a turu iya rayuwanka! Zan sa akama ka! Ka tabbattar da haka! Daga gari yaw aye zansa azo neman ka!” Alton yayi ihu, sai yajuya ya bubbuga kafa yatafi.

Thor bai damu kokadan da Altor ba, ko masu tsaronsa. Yana tunanin sarkin ne kawai. Ya tutture yan rundunan sai yajuya wa MacGil. Ya tutture mutane subar hanya yayinda ya hanzarta wa tebirin sarkin. Zuciyarsa nata jujjuyawa da tunani, kuma yagagara yarda da yadda abubuwa suka juya. Gashinan, daidai lokacinda tauraronsa yafara tashi, sai wani macijin buntu ya bata masa suna, ya samu ancuceshi an dauke masa masoyiyarsa. Kuma yanzu, gobe, barazanan daureshi a kurkuku. Kuma da sarauniya bata sonsa, yanasoron kar watakila hakan yafaru.q

Amma Thor bai damu da dukanin wannan ba yanzu. Duk abinda yadamesa shine kare sarkin.

Yakara turi da karfi yayinda yake saga hanyarsa cikin taron mutane, yacikaro da wani mai bada dariya, yawuce tacikin shirinsa, sai akarshe, bayan yakara turawa cikin masu hidima uku kuma, ya iya kaiwa tebirin sarkin.

MacGil ya zauna a sakiyan tebirin, wani babban tulun barasa a hanu daya, kumatunsa sunyi ja, yana dariyan nishadantarwan. Yana kewaye da duka manyan janarorinsa, sai Thor yasaya agabansu, ya tura yasamu hanya har zuwa gaban bencin, sanda akarshe, sarkin yaganeshi.

“Maigidana,” Thor yayi ihu, yanajin mstauwan dake muryarsa dakansa. “Dole nayi Magana dakai! Kayi hakuri!”

Wani mai tsaro yazo janye Thor, amma sarki yadaga tafin hanunsa.

“Thorgrin!” MacGil yayi ihu da mai zurfin, muryan sarakunansa, abuge da barasa. “Yaro na. Me yasa ka nufo tebirinmu? Tebirin yan runduna na can.”

Thor ya sunkuyar da kai kasakasa.

“Sarkina, kayi hakuri. Amma dole ne nayi Magana da kai.”

Wani mawaki yakada faranti a kunnen Thor, sai daga karshe, MacGil yayi nuni cewa ya daina. Wakan yayi shuru, sai duka janarorin suka juya suka kalli Thor. Thor yaji duka idanun da ke kansa.

“To, matashi Thor, yanzu filin naka ne. Kayi Magana. Menene da bazai iya jira zuwa gobe ba?” MacGil yace.

“Maigidana,” Thor yafara, amma yasaya. Menene zai fada daidai? Cewa yayi mafarki? Cewa yaga wata alama? Cewa yanajin za a bawa sarki guba? Zai zama maganan nada ma’ana?

Amma bashi da zabi. Dole ne yacigaba.

“Maigidana, nayi wata mafarki,” yafara. “Mafarkin akanka ne. a wannan zauren liyafan, a cikin wannan wurin. Mafarkin yakasance…cewa kada kasha barasa.”

Sarkin ya dago zuwa gaba, idanunsa suka budu da fadi.

“Cewa kada nasha barasa?” ya maimaita, ahankali kuma murya adage.

Sai, bayan wani dan lokaci na shurun mamaki, MacGil ya kwanta baya sai ya fashe da dariya, yana girgiza tebirin gabadaya.

“Cewa kada nasha barasa!” yasake maimaitawa. “Wannan wani irin mafarki ne! yakamata na kirashi sumbatu!”

Sarkin ya kwanta baya sai yayi ihu, sai dukan mutanensa suka shiga dariyan suma. Yanayin Thor yasauya, amma bazai iya komawa da baya yanzu ba.

MacGil yayi kira da hanu, sai wani mai tsaro yatako gaba ya kuma cafke Thor yafara tafiya dashi—amma Thor ya kufce da karfi daga rikon mai tsaron. Yariga ya daura zuciyarsa. Dole ya bawa sarki wannan bayanin.

Ka kare sarkinmu.

“Sarki na, ina bukatan ka saurara!” Thor yayi ihu, fuskansa jajazur, ya danna gaba sai ya buga hanunsa akan tebirin.

Dukan ya girgiza tebirin, sai dukan mutanen sarkin suka juya suka kalli Thor.

Shurun mamaki ya mamaye wurin, yayinda fuskan sarki ya sauya ya dauru.

“KANA bukata?” MacGil yayi ihu. “Baka bukatan komai daga wurina, yaro!” yayi ihu, haushinsa na karuwa.

Tebirin ya kara yin shuru, kuma Thor yaji kumatunsa sun zama ja da kunyatarwa.

“Sarki na, ka gafarce ni. Banso na rainaka ba. Amma na damu ne da lafiyanka. Kayi hakuri. Kada kasha barasa. Nayi mafarkin an baka guba! Kayi hakuri. Na damu dakai sosai. Dalilina na fadan haka kenan kawai.”

Ahankali, fuskar MacGil tasake. Ya kalli idanun Thor da zurfi sai yayi doguwar numfashi.

“Haka, ina iya ganin cewa ka damu. Koda ka kasance wawan yaro. Na yafe maka rashin ladabinka. Jeka yanzu. Kuma kada kasa na kara ganin fuskanka daganan zuwa safe.”

Ya kira masu tsaronsa da hanu, sai suka cafke Thor suka tafi dashi, dakarfi wannan karon. Sai tebirin ahankali takoma nishadinta yayinda duk suka koma shan barasansu.

Thor, da aka ja zuwa kafafu dayawa a can, yana konuwa da haushin. Yana soro saboda abubuwanda ya iakata anan daddaren nan, kuma yana jin cewa gobe shi zai ga sakamako. Watakila ma ace yabar nan. Har abada.

Yayinda masu tsaron ke masa turin karshe, Thor yasamu kansa a tebirin yan runduna, watakila kafa ashirin daga wurin sarki. Yaji wani hanu akan kafadansa sai yajuya yaga Reece asaye a wurin.

‘Nayita nemanka gabadaya yau. Menene yafaru dakai?” Reece ya tambaya. “Kana kama da kaga fatalwa!”

Thor ya rikice dayawa har yagagara mayar da martini.

“Zo ka zauna dani—na kama maka wurin zama,” Reece yace.

Reece yaja Thor zuwa gefensa azaune, a wani tebirinda aka ware wa iyalan sarki. Godfrey nadauke da barasa a kowani hanu, kuma Gareth na zaune a gefensa, yana kallo da idanu masu kiftawa. Thor yayi fata kan fata cewa Gwendolyn takasance a wurin, itama, amma bata nan.

 

“Menene, Thor?” Reece ya ingizashi, yayinda ya zauna a gefensa, “Kana hararan wannan tebirin Kaman zai cijeka.”

Thor ya girgiza kai.

“Idan nagaya maka, bazaka yarda ba. Saboda haka gomma na bar bakina arufe.”

“Gaya mani. Kana iya gaya mani komai,” Reece ya ingizashi da kaurin murya.

Thor yaga kallon dake cikin idonsa, sai yagane cewa, akarshe, wani na daukansa da muhimmanci. Yaja numfashi mai zurfi sai yafara. Bashi da wani asara.

“Wancan ranan, a cikin daji, tare da yar’uwanka, munga wani macijin whiteback. Tace wai alaman mutuwa ne, kuma na yarda haka ne. naje wurin Argon kuma ya tabbattar cewa mutuwa na zuwa. Bayan haka da kadan, nayi mafarkin cewa mahaifinka zai sha guba. Anan. Yau. A wannan zauren. Ina jinsa a cikin su kashina. Za a bashi guban. Wani na neman ya kasheshi,” Thor yace.

Ya fadi komai da sauri, ya kuma ji dadin sauke nauyin dake kirjinsa. Yaji dadin samun wani wanda ya ainihin kasa kunne.

Reece yayi shuru yayinda ya kalli cikin idanunsa na dogon lokaci. Akarshe, yayi Magana.

“Kayi kama da kafadi gaskiya. Bani da shakka. Kuma naji dadin damuwan da kayi da lafiyan mahaifina. Na yarda da magananka. Na yarda. Amma mafarku nada rikitarwa. Yawancin lokaci basu kasancewa yadda muke tunani.”

“Nagaya wa sarki,” Thor yace. “Kuma sunyi dariya na. tabbas, zai sha a daren nan.”

“Thor, nayarda kayi mafarkin nan. Kuma na yarda kana jin wannan. Amma nakanyi mugayen mafarku, nima, a gabadayan rayuwana. Wancan daren, nayi mafarkin an koreni daga fada, sai natashi inajin anyi haka. Amma ba a koreni ba. Ka fahimta? Mafarku abubuwan basabam bane. Kuma Argon yana Magana a habaicine. Bai kamata ka daukeshi da muhimmanci ba. Mahaifina na lafiya. Duka muna lafiya. kayi kokarin zama kasha’u ka sake. Kuma ka ji dadi.”

Da wannan, Reece ya jinginu a kujerarsa, arufe da barguna, yasha barasa. Ya kira wani mai hidima da hanu, wanda ya ajiye wani babban bangaren naman gada agaban Thor, tare da tulun shan barasa.

Amma Thor yazauna a wurin ne kawai, yana kallon abicinsa. Yaji duk duniyarsa gabadaya na narkewa akewaye dashi. Kuma baisan me yakamata yayi ba.

Yagagara tunanin komai banda mafarkinsa. Yayi Kaman kasance acikin sunbatu amma atashe, yazauna a wurin, yana kallon kowa na shayuwada kuma liyafa akewaye dashi. Abinda ya iyayi kawai shine ya kalli dukan barasan sha din, dukanin tulunan, masu nufan wurin sarki. Yana kallon kowani mai raba abinci da kyau, kowani tulun barasa. Duk lokacinda sarki ya kurba, Thor najin soro ajikinsa.

Thor ya matsu. Yagagara kallon wani wurin. Yayita kallo akan kallo na abinda yayi kama da sa’o’i.

Daga karshe, Thor ya hangi wani mai raba abinci na musamman wanda ya nufi sarki da wani tulunda ya bambamta da shauran. Yayi kato, an kuma yishi daga asalin gwal, arufe da adon duwatsun ruby da sapphire.

Daidai yake da tulun cikin mafarkin Thor.

Thor, zuciyansa na bugawa a cikin kirjinsa, ya kalla da tsoro yayinda mai rabawan ya kusanci sarki. Lokacinda yarage masa kafa daya kawai, Thor yagagara kara hakuri. Kowani ma’aunin jikinsa na ihun cewa wannan ne tulu mai guban.

Thor yayi tsalle daga tebirinsu, yatutture hanyarsa cikin taron jama’a mai kaurin, yana doke kowa dake kan hanyarsa da gwiwar hanunsa.

Daidai sarkin ya karbi tulun a hanunsa kenan, Thor yayi tsalle zuwa kan tebirinsa, ya mika hanu, sai ya doke wannan tulun daga hanun sarkin.

Jan numfashin soro ya cika zauren gabadaya yayinda tulun yayi tsalle sai ya diro akan dutse da wani babban kara.

Zauren gabadaya ya koma yayi shuru. Kowani maiwaka, kowani mai carafke, sun saya. Daruwan maza da mata duk sun juya suna kallo.

Sarkin yatashi ya harari Thor a kasa.

“Waye kai!” sarkin yayi ihu. “Kai yaro ami raini! Zan daureka a turu saboda wannan!”

Thor yasaya a wurin, yana soro. Yaji duniyan gabadaya na rushewa akansa. Yaso kawai shi yabace.

Babu sammani, wani kare yazo inda barasan ya zuba a kasa, sai ya lallashe duka. Kafin Thor ya mayar da martini, kafin dakin yafara motsi kuma, duka idanu sun koma kan Karen, wanda yafara wasu mununan, mara dadin jin ihu.

Bayan dan lokaci, Karen ya daskare sai ya fadi da gefe, amace. Dukan dakin sun kalli Karen da numfashin soro.

“Kasan barasan gubane!” wani murya yayi ihu.

Thor yajuya yaga yarima Gareth asaye a wurin, yazo zuwa gefen sarkin, yana mika yasar tukuma ga Thor.

“Yaya zaka iya sanin cewa ansa guba? Sadai idan kaine kasa! Thor yayi kokarin kasha sarki!” Gareth yayi ihu.

Taron jama’an gabadaya sun amsa da haushi.

Ku kaishi kurkuku,” sarki yabada ummurni.

Bayan dan lokaci, Thor yaji maso tsaro suna kamashi da karfi daga baya, suna janshi ta cikin zauren. Yana motsi yana son yayi tawaye.

“Babu!” yayiwo ihu. “Baku fahimta ba!”

Amma Babu wanda ya saurareshi. Anyashi ta cikin taron mutanen, da sauri, kuma yayin tafiya dashi, ya kalli yadda duk suka bace masa, yadda rayuwansa gabadaya yabace masa. Sun sallaka zauren da kuma wani kofan gefe, kofan ya rufu abayansu.

Nan yayi shuru babu hayaniya. Bayan dan lokaci, Thor yaji yana sauka. Hannaye dayawa na jansa a gangarawa murdadun matakalar dutse. Duhu nata karuwa bayan karuwa, sai jim kadan yafara sautin yan kurkuku.

Wani kofan dakin tsare mutane na karfe ya budu, sai ya fahimci inda ake kaishi. Kurkuku.

Yayi motsi, yana kokarin tawaye, kokarin ya kwufce.

“Baku fahimta ba!” yayi ihu.

Thor ya daga ido yaga wani mai tsaro ya tako zuwa gaba, wani babban, mara tausyin mutun da fuska mara samun gyara da kuma hakora masu launin kwai.

Ya harari Thor.

“Ai, na fahimta sosai,” muryarsa na barazana yazo.

Yaja hanunsa baya, sai abin karshe da Thor yagani ne hanunsa, yana kan saukowa tabbas wa fuskansa.

Sai duniyarsa ta bakance.